IQNA

23:43 - December 06, 2019
Lambar Labari: 3484297
Jaridar Sharq Alausat ta ce batun Isra’ila ne dailin da ya jawo rushewar tattaunawa tsakanin sarkin Morocco da Pompeo.

Kamfanin dillancin labaran IQNA, shafin jaridar Sharq Alausat ya bada rahoton cewa, batun Isra’ila ne dailin da ya jawo wargajear tattaunawa da ka ashirya yi tsakanin sarkin Morocco da Pompeo sakatare harkokin wajen Amurka.

Jaidar ta ce Mike Pompeo ya bukaci Morocco da mayar da alaka tsaaninta da Isra’ila kamar yadda take a 1994, amma sarkin Morocco ya yi watsi da wannan bukata.

Morocco ta bayyana cewa yanayin da ake ciki a 1994 da kuma yanzu yana da bambanci, kamar yadda kuma matakin kisan kiyashin da Isra’ila ta dauka kan falastinawa a 2000 ne ya jawo morocco ta yanke alaka baki daya da Isra’ila.

Amurka dai tana ta matsa lamba kan gwamnatin Morocco domin ta amince ta kulla wannan alaka da Israila domin hkan ya taimaka ma Netanyahu wanda yake cikin matsala a halin yanzu.

 

 

https://iqna.ir/fa/news/3862102

 

 

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: iqna ، kamfanin dillancin labaran iqna ، morocco ، sarkin morocco ،
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: