IQNA

12:04 - December 22, 2019
Lambar Labari: 3484337
Musulmin yankin San Martin a Amurka sun samu izinin gina masallaci bayan jira na shekaru 13.

Kamfanin dillancin labaran IQNA, shafin sanfrancisco.cbslocal ya bayar da rahoton cewa; bayan jira na shekaru 13 musulmin yankin San Martin a Amurka sun samu izinin gina masallaci da makabarta, a wani wuri da ska saya mai fadin hekta 5.67.

Tun a cikin shekara ta 2016 ce dai musulmin yankin suka sayi wannan wuri, da nufin gina masallaci a matsayin babbar cibiyarsu ta addinin muslunci da kuma makabarta.

Wannan shiri dai ya fuskanci tsaiko, sakamakon yadda wasu mazauna yankin suka yi ta nuna rashin gamsuwarsu da hakan, wanda hakan yasa aka kwashe tsawon shekaru ana jira.

Musulmin yankin dai sun kashe kudi kimanin dala miyan 3 a wurin saye da kuma tsara yadda ginin wrin zai kasance.

An kwashe tsawon shekaru musulmin wanna yankin da ke cikin jihar California, suna gudanar da harkokinsu ne a cikin wani babban suto na jiyar kaya, duk kuwa da cewa adadin mutanen yankin bai wuce dubu 10 ba.

 

https://iqna.ir/fa/news/3865487

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: