IQNA

An Yi Allawadai Da Kai Hari Kan Masalatai A Ethiopia

14:29 - December 22, 2019
Lambar Labari: 3484338
Abi Ahmad Ali Firayi ministan Ethiopia  ya yi Allawadai da kai hari kan masallatai a kasar.

Kamfanin dillancin labaran IQNA, Abi Ahmad Ali Firayi ministan Ethiopia ya yi kakkausar suka da Allawadai da kai hari kan masallatai, kamar yadda kuma mahukunta a kasar Ethiopia suka sanar da kame wasu mutane biyar da ake zargi da kai hare-hare kan wasu masallatai guda hudu a yankin Amhara na kasar.

Yayin da yake sanar da hakan kakakin gwamnatin jihar Amharan Getnet Yirsaw jami’an tsaro sun sami nasarar kame mutane biyar din da ake zargi da shiryawa da kuma kai wadannan hare-hare kan masallatan da kuma kona su.

Baya ga masallatan da aka kai wa hare-haren, har ila yau an kai wasu hare-hare kan wasu wajajen kasuwanci na musulmi a wannan yankin lamarin da ake ganinsa a matsayin wani kokari na haifar da fitina da rikici na addini a yankin, bisa la’akari da wasu hare-hare makamantan hakan da aka kai wasu coci-coci a yankin.

Har ya zuwa yanzu dai ba a tantance manufar masu kai wadannan hare-haren ko kuma wadanda suke dauka nauyinsu ba, sai dai firayi ministan kasar Abiy Ahmad ya sha alwashin cewa ba zai taba barin masu tsaurin ra’ayin addini su haifar da fitina a kasar ba.

Wasu dai suna zargin wasu manyan kasashen duniya da hannu cikin irin wadannan hare-hare bisa la'akari da kaurin sunan da wasu kasashen suka yi wajen haifar da fitina na kabilanci da addini da nufin samun damar yin kutse da cimma manufofinsu a wadannan kasashe na Afirka da sauran kasashe masu tasowa.

 

 

https://iqna.ir/fa/news/3865747

captcha