IQNA

14:58 - December 26, 2019
Lambar Labari: 3484347
Jagoran mabiya kiristocin darikar katolika ya bayyana haihiuwar annabi Isa (AS) a matsayin rahmar ubangiji.

Kamfanin dillancin labaran IQNA, shafin tashar France 24 ya bayar da rahoton cewa, a lokacin da yake gabatar da jawabin kirsimati a fadar Vatican, Paparoma Francis jagoran mabiya kiristocin darikar katolika ya bayyana haihiuwar almasihu a matsayin rahmar ubangiji ga dukkanin talikai.

Ya ci gaba da cewa; duk da irin barna sabo da bayi suke yi, amma duk da haka ubangiji yana kwararo rahamarsa da falalarsa a gare su, ba tare da ya dauki fansa a kansu saboda sabon da suke yi, wannan jin kai ne na ubangiji.

Haka nan kuma ya yi tsokaci dangane da ayyukan assha da wasu limamani kirista suke yi a fadar Vatican, tare da bayyana cewa lokaci ya yi da irin wannan yanayi zai kawo karshe, kamar yadda kuma ya karrama wasu yara daga kasashen Venezuela, Iraki da kuma Uganda a taron kirsimati.

 

 

https://iqna.ir/fa/news/3866491

 

 

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: