IQNA

21:17 - December 28, 2019
Lambar Labari: 3484354
Wani harin kunar bakin wake a Mugadishou Somalia ya yi sanadiyyar mutuwar mutane da dama.

Kamfanin dillancin labaran IQNA, tashar Russia today ta bayar da rahoton cewa, da safiyar yau ne aka kai wani mummunan harin bam a yankin Afgui da ke kudancin birnin Mugadishou na Somalia, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mutane masu yawa.

Rahoton ya ce harin an kunar bakin wake ne, kuma daga cikin wadanda suka mutu akwai Turkawa 4 a cikinsu.

Umar Filis shi ne magajin garin birnin, ya bayyana cewa akwai daliban jami’ar Banadir masu yawa tsakanin wadanda suka mutu.

Haka nan kuma rahoton ya ce an kai harin ne a lokacin da mutane suke ta kai komo da safiyar yau domin tafiya harkokinsu.

Har yanzu dai babu wani utum ko wata kungiya da ta dauki nauyin harin, amma tuni aka nuna yatsun tuhuma ga ungiyar Alshabab mai bin akidar salafiyya, wadda ke da alaka da kungiyar alkaida.

 

 

https://iqna.ir/fa/news/3867036

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: