Kamfanin dillancin labaran IQNA, kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Sayyid Abbas Musawi ya mayar da kakkausan martani dangane da tsoma baki da gwamnatin Faransa ta yi a cikin harkokin Iran na cikin gida, musamman dangane da kame wata ba’iraniya mai suna Adelkha, wadda ake zarginta da gudanar da ayyukan liken asisri ga kasashen ketare.
Haka nan kuma dangane da batun wani dan kasar Faransa da aka kame a cikin Iran, hakan ya faru ne bayan saunsa da hannu dumu-dumu a cikin yunkurin haifar da matsalar tsaro a cikin kasar ta Iran, kuma lauyansa yana da masaniya kan komai.
Musawi ya kara da cewa, yada karairayi a fagage na siyasa ko kafofin yada labarai, ba zai hana Iran daukar mataki na shari’a a kan wadanann mutane ba.
https://iqna.ir/fa/news/3867312