IQNA

15:41 - January 01, 2020
Lambar Labari: 3484366
Daya daga cikin malaman makarantun kur’ani a Najeriya ya yi kira ga masu hali da su taimaka ma Wadannan makarantu.

Kamfanin dillancin labaran IQNA, shafin jaridar Daily Trust ya bayar da rahoton cewa, Alhaji Garba Abubakar Ibrahim shugaban wata makarantar kur’ani a Kaduna, ya kirayi masu hali daga cikin musulmi da su taimaka wajen ayyukan wadannan makarantun.

Wannan kira ya zo ne a lokacin gudanar da wani bikin yaye wasu daga cikin dalibai da suka kammala karatu.

Malam Ibrahim ya ce; ana samun gagarumin ci gaba wajen karatu da kuma karuwar dalibai masu karatun, to amma matsala guda da ake fuskanta ita ce, babu isassun kudaden tafiyar da wadannan makarantu da kuma daukar nauyin daliban.

Makarantun allo dai a Najeriya su ne makarantu na farko da aka sania  tsarin koyar da kur’ani mai tsarki, kafin samun wasu sabbin hanyoyi na zamani.

 

https://iqna.ir/fa/news/3868114

 

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: