IQNA

11:10 - January 02, 2020
Lambar Labari: 3484369
Gwamnatin Amurka ta sanar da dakatar da dukkanin ayyukan ofisin jakadancinta a birnin Bagadaza na Iraki.

Kamfanin dillancin labaran IQNA, tashar Almanar ta bayar da rahoton cewa, a jiya Ofishin jakadancin Amurka ya sanar da dakatar da dukkanin ayyukan ofishin kasar da ke birnin Bagadaza, inda ake sa ran dauke wasu ayyukan zuwa wani yanki.

Rahoton ya kara da cewa, Amurka ta dauki wannan matakin ne bayan da al’ummar kasar ta Iraki suka kone ofishin jakadancin an Amurka da ke birnin Bagadaza, inda jakadan na Amurka ya sha da kyar, sakamakon harin da Amurkan ta kai a kan dakarun sa kai na al’ummar Iraki.

Ofishin jakadancin an Amurka ya ce zai mayar da wasu daga cikin ayyukans zuwa birnin Arbil.

 

https://iqna.ir/fa/news/3868354

 

Abubuwan Da Ya Shafa: iqna ، kamfanin dillancin labaran iqna ، Iraki ، Bagadaza ، Arbil
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: