IQNA

7:35 - January 06, 2020
Lambar Labari: 3484381
Babban malamin addini na kasar Iraki Ayatollah Sayyid Ali Sistani ya aike da sakon ta’aziyya zuwa ga jagoran juyin juya hali na kasar Iran.

Kamfanin dillancin labaran Iqna ya bayar da rahoton cewa, a jiya Ayatollah Sistani ya aike da rubutaccen sakon ta’aziyyar shahadar Janar Qassem Sulaimani zuwa ga jagoran juyin juya hali Ayatollah Sayyid Ali Khamenei.

Ga matanin sakon kamar haka;

Da sunan Allah mai rahma mai jin kai

Mu ga Allah muke kuma zuwa gare shi ne za mu koma.

Mai Girma Ayatollah Khamenei

Assalamu Alaikum wa rahmatullah

Samun labarin shahadar bababn gwarzo Haji Qassem Sulaimani ya saka mu cikin bakin ciki matuka.

Hakika ya bayar da gagarumar gudunmawa wajen fatattakar mayakan ‘yan ta’addan Daesh daga Iraki, ya yi gagarumin aiki da hidima mai yawa ga Iraki tsawon shekaru, wanda al’ummar kasar ba za su taba mantawa da hakan ba.

Ina mika sakon ta’aziyya kan wannan baban rashi gare ka da kuma dukkanin iyalansa da al’ummar Iran baki daya, musamman al’ummar lardin Kerman.

Ina rokon Allah da ya yi masa rahma da gafara, mu kuma ya kyautata karshenmu.

Babu duba ko wani karfi sai ga Allah mai girma da daukaka.

Sayyid Alhussaini Sistani

8 Jumada Awwal – 5 – 1 - 2020

 

Abubuwan Da Ya Shafa: iqna ، Ayatollah Sistani ، ، ،
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: