Kamfanin dillancin labaran IQNA ya bayar da rahoton cewa, nan da ‘yan sa’oi masu zuwa ne za a gudanar da sallar janaza ga gawar shahid Sulaimani a masallacin juma’a na jami’ar Tehran.
Rahoton ya ce jagoran juyin juya’ halin muslunci na kasar Iran ne zai jagoranci sallar janazar a kan gawar Sulaimani tare da wadanda suka yi shahada tare da shi.
Tun bayan isowar gawarsa a jiya a biranan Mashhad da Ahwaz na kasar Iran aka yi gangami na miliyoyin jama’a domin tarbar gawar, da jijjifin safiyar yau kuma gawawwakin sun iso birnin Tehran.
A nata bangaren Zainab Sulaimani diyar Kasim Sulaimani ta fadi a wajen taron janazar kafin yi ma mahaifinta salla cewa, ya kasance mutum ne mai kwazo da yawan ibada da kuma kaskantar da kai, kamar yadda ya kasance mutum ne yana fatan yin shahada a karshen rayuwarsa.
Wannan taaron janazar dai yana samun halartar mutane daga ciki da wajen kasar Iran, kamar yadda miliyoyin Iraniyawa daga sassa daban-daban na kasar suke ta isowa birnin Tehran domin halartar wannan janaza a halin yanzu haka.
https://iqna.ir/fa/news/3869404