IQNA

Abdulmahdi Ya Ce Sun Samu Sako Daga Sojojin Amurka Kan Fara Ficewarsu Daga Iraki

22:32 - January 07, 2020
Lambar Labari: 3484391
Firayi ministan Iraki ya bayyana cewa sun samu sako daga rundunar sojin Amurka kan shirinta na ficewa daga Iraki.

Kamfanin dillancin labaran IQNA, kamfanin dillancin labaran  Saumaria News ya bayar da rahoton cewa, Adel Abdulmahdi firayi ministan Iraki ya tabbatar da cewa sun samu sako daga sojin Amurka da ke Iraki kan shirinsu na ficewa daga kasar.

Ya ce sojojin na Amurka sun kauce daga abin da aka cimma yarjejeniya da su, inda aka yi yarjejeniya da su kan yaki da Daesh, amma yanzu sun shiga wani abu daban.

Abdulmahdi ya kara da cewa, an amince da wannan kudiri na ficewar sojojin waje da suka hada da Amurka ne, saboda hakan shi kadai ne mafita, domin kuwa Irakawa sun rayu a tsakanin 2011 zuwa 2014 ba tare da Amurkawa ba har zuwa lokacin da aka turo ‘yan ta’adda a kasar.

 

 

https://iqna.ir/fa/news/3870106

captcha