IQNA

23:01 - January 13, 2020
Lambar Labari: 3484409
Kungiyar OIC ta yi Allawadai da harin  da aka kai a masallaci a ranar Juma’a a garin Kuita na Pakistan.

Kamfanin dillancin labaran IQNA, Yusuf Alusaimin shugaban kungiyar kasashen musulmi ta OIC ya ce; kungiyar tana yin Allawadai da kakkausar murya dangane da harin ta’addancin aka kai a masallaci a ranar Juma’a a garin Kuita na Pakistan wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mutane.

Ya ce hakika wannan hari abin ban takaici ne, kuma dukkanin al’ummomin musulmi suna yin Allawadai da hakan.

Haka nan kuma ya kara da cewa, al’ummar Pakistan al’umma guda ce, kuma ta’addancin ‘yan ta’adda ba zai raba sub a.

Ya ce babu wani dalili a cikin addinin muslunci da ya halasta ma wani day a kai hari ya kasha mutane babu gaira babu sabar.

A ranar Juma’a da ta gabata ce wani ta’adda ya tarwatsa kansa a cikin masallacin Juma’a a lokacin sallar Juma’a, inda ya kasha tare da jikkata mutane da dama.

 

https://iqna.ir/fa/news/3871190

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: iqna ، kamfanin dillancin labaran iqna ، kara ، wanann hari ،
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: