IQNA

22:43 - January 15, 2020
Lambar Labari: 3484418
Shugaban kasar Iran Hassan Rauhani ya bayyana Qasem Sulamainia  matsayin gwarzon al’ummomi raunana.

Kamfanin dillancin labaran IQNA ya bayar da rahoton cewa, a yau ne firayi ministan kasar Syria Imad Khamis ya gana da shugaban kasar Iran Hassan rauhania birnin Tehran fadar mulkin kasar Iran.

A yayain ganawar tasu bangarorin biyu sun tattauna batutuwa da suke da alaka da halin da ake cikia yankin gabas ta tsakiya, da kuam alaka tsakanin kasashen biyu aminan juna.

Shugaba Rauhani ya jaddada cewa kasashen Iran kasashe ne masu dadden kawance na tarihi, wada kuma duk wani matsin lamaba ba zai iya kawo karshen wanann kawance ba.

Shi ma a nasa bangaren firayi ministan kasar ta Syri ya yaba da irin tsayin dakan da Iran ta yi wajen taimaka kasar Syria domin yaki da ‘yan ta’adda wadanda aka turo da nufin rusa kasar.

Ya ce shahid Kasim Sulaimani ya taka gagarumar rawa wajen murkushe ‘yan ta’adda a Syria, a kan haka al’ummar Syria ba za su taba mantawa da kwazon da ya yi wajen kubutar da kasarsu ba.

 

 

https://iqna.ir/fa/news/3871641

Abubuwan Da Ya Shafa: iqna ، kamfanin dillancin labaran iqna ، ، ، ،
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: