IQNA

20:30 - January 19, 2020
Lambar Labari: 3484432
Bangaren kasa da kasa, ana gudanar da zaman tattaunawa hanyoyin sulhunta masu rikici a Libya a birnin Berlin.

Kamfanin dillancin labaran IQNA, tun a jiya ne tawagogi daga kasashen duniya daban-daban suka fara isa birnin na Berlin, domin halartar zaman taron, wanda shugabar gwamnatin kasar Jamus za ta jagoranta tare da halartar Rasha, Turkiya, Aljeriya, UAE, Masar, Faransa, Birtaniya, China da Amurka.

A jiya ne shugabar gwamnatin kasar ta Jamus ta fara gudanar da tattaunawa tare da bangarori daban-daban, dangane da zaman taron, da nufin ganin an samu hanyar warware rikin kasar ta Libya.

Gassan Salamah wakilin musamman na majalisar dinkin duniya a kasar Libya wanda ya isa birnin na Berlin ya bayyana cewa, halin da ake ciki a kasar ta Libya yana da matukar tayar da hankali

Haka nan kuma ya kara da cewa akwai bukatar kasashen ketare su daina yin katsalandan a cikin harkokin kasar ta Libya matukar ana bukatar samar da zaman lafiya mai dorewa a kasar ta Libya.

 

 

 

https://iqna.ir/fa/news/3872556

Abubuwan Da Ya Shafa: iqna ، kamfanin dillancin labaran iqna ، Libya ، Jamus ، katsalandan ، dorewa
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: