IQNA

22:04 - January 20, 2020
Lambar Labari: 3484436
Rafael Wasil shugaban majami’ar Azra da ke garin Dikranis ya sumbaci hannun Sheikh Taha Al-Nu’umani.

Kamfanin dillancin labaran IQNA, shafin yada labarai an Misri yaum ya bayar da rahoton cewa, al’ummar garin Dikranis sun yi mamaki matuka kan yadda malamin kiristan ya sumbaci hannun sheikh Taha al-Nu’umani bayan sauraren karatunsa na kur’ani.

Rahoton ya ce malamin kiristan ya halarci wani wurin ta’aziyya ne, inda sheikh Taha Al-Nu’umani yay i karatun kur’ani, bayan gama karatun, malamin kiristan ya mike ya nufi wurinsa ya sumbaci hannunsa da goshinsa.

Sheikh Nu’umani ya bayyana cewa, wannan babbar alama ce ta kaskantar da kai da kauna da girmamawa ta wannan malamin kirista ga musulmi.

https://iqna.ir/fa/news/3872726

 

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: iqna ، kamfanin dillancin labaran iqna ، Masar ، musulmi ، kirista
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: