IQNA

23:23 - January 22, 2020
Lambar Labari: 3484439
Ana ci gaba da zaman taron waya da kai kan addinin muslunci a jami’ar Mount Royal da ke Canada.

Kamfanin dillancin labaran IQNA, daliban jami’a musulmi ne suka shirya zaman taron a jami’ar ta Mount Royal da ke kasar Canada, domin wayar da kan sauran dalibai dangane da addinin musulunci.

Tun a ranar 20 ga watan janairu ne aka fara taron wanda za a kammala a ranar 24ga wannan wata na Janairu, inda ake gabatar ad laccoci dangane da matsaloli da suke fuskantar msulmi a kasar da ma wasu kasashen turai.

Dilly Hussain na daga cikin wadanda suka shirya taron, ya bayyana cewa babbar manufarsu ita ce wayar da kan jama’a kan su gane cewa addinin muslunci addini ne na zaman lafiya da fahimtar juna da kuma girmama dan adam, ba ta’addanci ba kamar yadda suke zato.

 

 

https://iqna.ir/fa/news/3873280

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: