Kamfanin dillancin labaran IQNA, shafin jaridar Alakhbar ya sheda cewa, Amurka ta ja sabuwar daga da sabuwar gwamnatin kasar Lebanon.
Rahoton ya ce a zantawarsa da wasu kafofin yada labarai, Mike Pompeo sakataren harkokin wajen Amura ya bayyana cewa, sharadin taimaka ma gwamnatin Lebanon shi ne sauraren bukatun al’ummar kasar Lebanon.
Ya ce zanga-zangar da mutane suke yia Beirut ita ce neman gwamnati ta yanke alaka da kungiyar Hizbullah, saboda haka wannan bukatar da ya kira ta mutane ita e Amurka tak bukata kafin bayar da duk wani taimako ga gwamnatin Lebanon.
Wannan matakin yana zuwa ne a daidai lokacin da majalisar dinkin duniya da kungiyar tarayyar turai suka nuna cikakken goyon bayansu ga sabowar gwamnatin ta Lebanon.
https://iqna.ir/fa/news/3873694