IQNA

Mutanen Iraki Sun Fara Daukar Matakan Fitar Da Amurka Daga Kasar

22:47 - January 25, 2020
Lambar Labari: 3484449
Taqi Amirli wakili daga gungun Fatah a majalisar Iraki ya ce sun fara daukar matakai na doka domin fitar da Amurkawa.

Kmafanin dillancin labaran IQNA ya habarta cewa, wakili daga gungun Fatah a majalisar dokokin Iraki ya tabbatar da cewa, a halin yanzu sun fara daukar dukkanin matakai da suka dace domin fitar da Amurka daga Iraki ta hanyoyi na dokar kasa.

Dangane da yaduwar kungiyoyin ‘yan ta’adda kuwa ya ce Amurka ce ita ce da kanta ta kawo kungiyar ‘yan ta’adda da Daesha  cikin Iraki a shekara ta 2014 wato shekaru shida da suka gabata.

Sannan kuma ya yi ishara da masu tunanin cewa Amurka za ta iya kawo tsaro a Iraki, inda ya ce abin da ya faru ya tabbatar da cewa Amurka ba ta son zaman lafiya a kasar.

Dangane da hakan ya ce kamar yadda Irakawa ne da kansu suka kori ‘yan ta’addan daesh ba Amurkawa ba, a wannan karon ma Irakawa ne da kansu za su fitar da Amurkawa daga kasar ta Iraki.

 

 

https://iqna.ir/fa/news/3874019

 

 

captcha