IQNA

19:47 - January 28, 2020
Lambar Labari: 3484459
Amurkawa da dama ne suka gudanar da jerin gwano domin nuna rashin amincewa da sabuwar dokar gwamnatin India da ke nuna wariya ga musulmi.

Kamfanin dillancin labaran Iqna, kungiyoyin farar hula ne na kasar Amurka suka kirayi jerin gwanon a birnin New York, wanda ya samu halartar dubban jama’a.

A yayin jerin gwanon an daga kwalaye da aka yi rubutu a kansu, da ke kira ga gwamnatin India da ta kawo karshen nuna wariya ga musulmi a kasar.

Haka nan kuma masu jerin gwanon sun yi gangami a gaban karamin ofishin jakadancin India da ke birnin New York, domin isar da sakonsu kai tsaye ga mahukuntan kasar ta India.

Zanga-zangar ta samu halartar musulmi da wadanda ba musulmi, da kungiyoyi masu zaman kansu da lauyoyi masu fafutuka da sauransu.

 

https://iqna.ir/fa/news/3874693

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: