IQNA

22:50 - January 28, 2020
Lambar Labari: 3484460
A daren yau Talata an gudanar da zaman makoki na tunawa da zagayowar lokacin wafatin fatimam Zahra a Husainiyar Imam Khomenei (RA).

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a daren yau an gudanar da zaman makoki na tunawa da zagayowar lokacin wafatin Sayyida Fatima Zahra (SA) a Husainiyar marigayi Imam Khomeini da ke birnin Tehran, tare da halartar jagoran juyin juya halin muslunci, inda Hojjatol Islam Rafi’i ya gabatar da jawabi kan tarihin rayuwarta da kuma irin gudunmawar da ta bayar wajen gina al’ummar al’ummar musulmi.

Baya ga haka kuma ya tabo irin kyawawan halayenta da kuma bautar ubangiji, kamar yadda a bangaren dabi’unta ya buga misalai da suke abin koyi ga dukaknin musulmi, wanda suke dabi’u ne da ta koya daga mahaifinta manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da alayensa tsarkaka.

A daya bangaren Maisam Muti’i ya karanta makokin wafatinta ga dubban mahalarta wurin.

 

https://iqna.ir/fa/news/3875017

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: