IQNA

23:02 - January 30, 2020
Lambar Labari: 3484464
A daren yau an gudanar da zaman makoki na karshe na tunawa da zagayowar lokacin wafatin Sayyid Fatima Zahra (AS) a Husainiyar Imam Khomeni (RA)

Kamfanin dillancin labaran IQNA, a daren yau ne aka gudanar da zama na karshe na juyayi da makokin zagayowar lokacin wafatin Sayyida Fatima Zahra AS) a Husainiyar marigayi Imam Khomeni, tare da halartar dubban jama’a da suka hada da manyan jami’an gwamnati, da jami’an soji.

Hojjatol Islam Khatami ne ya gabatar da jawabi a wurin, inda ya tabo kadan daga cikin irin gudunmawar da Sayyida Zahra (AS) ta bayar wajen daukaka Kalmar Allah, da kuma irin sadaukantawar da ta yi a sahun gaba domin wanzuwar addinin Allah madaukakin sarki.

Hojjatol Islam Khatami ya bayyana cewa, babban sirrin sadaukarwar mabiya ahlul bait na tattare da yin koyi ne da koyarar manzon Allah da alayensa, wanda kuma Fatima Zahra ita ce kan gaba tare da mijinta wajen isar da wannan koyarwa irin ta manzon Allah ga al’ummar musulmi.

Daga karshe Mahdi Samawati ya karanta addu’ar tawassul, kamar yadda kuma Saeed Haddafiyan ya karanta makokin wafatinta.

 

https://iqna.ir/fa/news/3875295

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: