IQNA

Shugaban Aljeriya Ya Yi Watsi Da Yarjejeniyar Karni

23:59 - February 02, 2020
Lambar Labari: 3484477
Bangaren kasa da kasa, Shugaban kasar Aljeriya ya bayyana cewa sun cimma matsaya guda tare da takwaransa na Tunisia kan yin watsi da yarjejeniyar karni.

Kamfanin dillancin labaran IQNA, shafin Almayadeen ya bayar da rahoton cewa, Abdulmajid tabun shugaban kasar Aljeriya ya bayyana cewa, ba za su taba amincewa da tsarin da Trump ya gabatar kan makomai Falastinu ba, domin sun san da zaman falastinu ne kawai a kan iyakokinta na 67 da babban birninta Quds.

Ya ce sun cimma matsaya tare da Qais Sa’id shugaban kassar Tunisia  akan wannan batu, kuma matsayar za ta kasance day ace tare da kasar Tunisia a kan wannan lamari.

Ko a jiya dubban mutane ne ska gudanar da jerin gwano a dukkanin biranan kasar Aljeriya domin yin watsi da wanann shiri, tare da jaddada goyon bayansu ga al’ummar Falastinu.

Donald Trump ya gabatar da shirin nasa da ake kira da yarjejeniyar karni da sunan kawo sulhu tsakanin yahudawan Isra’ila ‘yan share wuri zauna da kumafalastinawa da aka kwace ma kasa, inda shirinsa ya amine da samuwar Isra’ila a hukumance, kuma falastinawa za su kasance karkashin daular Isra’ila, amma za asakar musu mara kan wasu lamurra, sai dai babu kasar Falastinu mai cin gishin kanta.

 

https://iqna.ir/fa/news/3876037

captcha