IQNA

23:52 - February 04, 2020
Lambar Labari: 3484484
Wasu daga cikin larabawa da masu fafutuka a Amurka sun yi gangamin kin amincewa da yarjejeniyar karni a Dalas.

Kamfanin dillancin labaran IQNA ya bayar da rahoton cewa, daruruwan mutane ne suka fito kan tituna a birnin Dalas na kasar Amurka, domin nuna rashin amincewarsu da abin da ake kira shirin Trump na yarjejeniyar karni.

masu gangamin sun hada da larabawa mazauna kasar Amurka, da kuma masu rajin kare hakkokin bil adama, awadanda suke bayyana shirin zaman lafiya da Trump ya gabatar tsakanin Isra'ila da falastinawa da cewa babu adalcia  cikinsa.

Masu gangamin sun bukaci gwamnatin Amurka da ta sake yin nazari kan wannan shiri na Trump, wanda suke kallonsa  matsayin wani babban abin kunya ga kasar, wanda kuma zai iya zubar da mutuncinta.

 

 

https://iqna.ir/fa/news/3876442

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka: