IQNA

23:51 - February 05, 2020
Lambar Labari: 3484489
Shugabar majalisar wakilan Amurka ta yada takardun jawabin Trumpa  gaban majalisar dokoki.

Kamfanin dillancin labaran iqna, shugabar Majalisar Wakilan Amurka Nancy Pelosi, ta kekketa takardar jawabin shugaba Donald Trump bayan ya kammala jawabinsa kan halin da kasa ke ciki a zauren majalisar kasar.

Wannan dai ya biyo bayan da Trump din, ya yi watsi da ita Pelosin a lokacin da ta mika masa hannu, wanda ake ganin hakan ne ya harzuka ta ta dau wannan matakin na walakanta shi a idon duniya.

A yayin jawabin nasa, shugaba Trump ya kauce wa batun dambarwar tsige shi.

Sai kuma wasu batutuwan da suka hada da yake-yaken Amurka a wasu kasashen duniya da shirin janye dakarun kasar daga Afghanistan.

A wannan Larabar ce ake sa ran majalisar dattawan Amurkar wadda jam'iyyar Republican ke da rinjaye a cikinta, za ta bayyana matakinta kan bukatar tsige shugaba Trump da aka gabatar mata bisa zargin yin amfani da karfin ikonsa ta hanyar da ba ta dace ba.

 

 

https://iqna.ir/fa/news/3876656

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka: