IQNA

23:58 - February 11, 2020
Lambar Labari: 3484512
Sarakunan Oman da Jordan sun aike da sakonni zuwa ga shugaban kasar Iran domin taya al'ummar kasar murnar bukukuwan ranar juyi.

Kamfanin dillancin labaran IQNA, shafin yada labarai na tashar alalam ya bayar da rahoton cewa,  Haisam bin Tariq sarkin kasar Oman, ya aike da sakon wasika zuwa ga shugaba Rauhani na Iran, domin taya shi murnar cikar shekaru 41 da samun nasarar juyin juya halin muslunci a kasar.

Shi ma a nasa bangaren sarkin kasar Jordan Abdullah na biyu, ya aike ad nashi sako zuwa ga shugaba Rauhani, inda ya mika sakon taya murna gare shi da kuma al'ummar Iran, na cikar shekaru 41 da samun nasarar juyi, tare da yin fatan alhairi ga dukkanin al'ummar kasar.

Kafin haka dai sarakunan kasashen Kuwait da Qatar da ma shugabannin kasashe da dama, sun aike wa shugaba Rauhani da irin wadannan sakonni.

 

 

 

https://iqna.ir/fa/news/3878210

Abubuwan Da Ya Shafa: iqna ، kamfanin dillancin labaran iqna ، sarakuna ، Oman ، Jordan ، sako ، Iran
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka: