IQNA

23:49 - February 12, 2020
Lambar Labari: 3484513
Abbas Musawi ya bayyana cewa Iran za ta kare manufofinta a cikin kasarta da ma duk inda ya dace kuma za ta mayar da martani kan masu shishigi.

Kamfanin dillancin labaran IQNA,

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran Sayyid Abbas Musawi ya bayyana cewa, Iran za ta mayar wa Isra’ila da mummunan martani matukar ta nemi ta yi wani shishigi a kan kasar ta Iran.

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar ta Iran Sayyid Abbas Musawi ya bayyana haka ne a yammacin jiya laraba, a lokacin da yake mayar da martani kan barazanar da ministan yakin Isra’ila ya yi, kan cewa suna yaki da Iran a  cikin Syria da nufin raunana ta.

Musawi ya ce, Iran ba za taba yin kasa a gwiwa ba wajen kare manufofinta, kuma kasantuwarta a Syria ya zo ne bisa ga gayyata ta halastacciyar gwamnatin Syria, wanda hakan bai sabawa wata doka ta duniya ba.

Ya ci gaba da cewa, Iran za ta mayar da martani ba tare da wata tababa ba, a kan Isra’ila ko kan duk wani wanda ya yi shishshigi a kanta,a  cikin Syria ne ko kuma a wani wuri na daban.

 

 

https://iqna.ir/fa/news/3878502

Abubuwan Da Ya Shafa: iqna ، kamfanin dillancin labaran iqna ، Sayyid Abbas Musawi ، ،
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka: