IQNA

20:52 - February 13, 2020
Lambar Labari: 3484517
Dakarun Hasd Al-sha’abi sun yi kira zuwa taron tunawa da cikar kwanaki 40 da kisan janar Kasim Sulaimani da Abu mahdi Almuhandis.

Kamfanin dillancin labaran IQNA ya bayar da rahoton cewa, dakarun sun yi kira ne ga dukaknin al’ummar Iraki da su fito gobe domin tunawa da cikar kwanaki arba’in da kisan janar Kasim Sulaimani da Abu mahdi Almuhandis wanda za a gudanar a makabartar Wadissalam a Najaf.

Dakarun hashd Al-sha’abi sun samar da dukkanin abubuwan da ake bukata na zirga-zirga zuwa da dawowa daga garuruwa daban-daban zuwa wannan taro.

Baya ga haka kuma, za  agudanar da irin wannan taroa  wasu lardunan kasar, da suka hada da Bagdad, Babul, Karbala, Muthanna, Diwaniyya, Ziqar, Wasit, Misan, Basara da saurasu, inda za a tuna da cikar kwanaki arba’in da kisan manyan kwamandodin da suka murkushe ‘yan ta’adda a Iraki, wadamda su kuma Amurka ta kashe su.

 

https://iqna.ir/fa/news/3878597

Abubuwan Da Ya Shafa: iqna ، kamfanin dillancin labaran iqna ، taro ، ، ،
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka: