IQNA

An Yaba Da Kame Mutumin Da Ya Yi Kokarin Kai Hari Kan Coci A Kaduna

23:53 - February 17, 2020
Lambar Labari: 3484530
Tehran – IQNA, kungiyoyin kare hakkin bil adama a Najeriya sun yaba wa jami’an tsaro kan cafke mutumin da ya dana bam a coci a Kaduna bayan an zargi musulmi kan hakan.

Rahotanni daga Najeriya sun ce, kungiyoyin kare hakkin bil adama a kasar sun bayyana kame mutumin da ya dana bam a coci a Kaduna da cewa mataki ne mai kyau da ya kamata a yaba wa jami’an tsaro kansa.

Bayan yunkurin kai harin bam din a kan coci mabiya addinin kirista a Kaduna, kungiyar kiristocin Najeriya ta yi zargin cewa ana kokarin kashe kiristoci, yayin da wasu kuma suka gudanar da zanga-zanga a Lagos suna zargin musulmi da yin haka, duk da cewa wasu sun zargi Boko Haram ne.

Amma bayan bicike da bin diddigin lamarin da jami’an ‘yan sanda suka yi, sun gano mutumin da ya dana bam din a coci, mai suna Nathaniel Samuel, wanda shi ma mabiyin addinin kirista ne.

Bayanin ya ce wannan ya kara tabbatar da cewa masu hankoron haddasa fada da rashin jituwa a tsakanin musulmi da kirista a Najeriya wasu mutane ne da suke gudanar da wani aiki domin cimma wata manufa da kuma samun abin duniya.

Mabiya addinan biyu dai suna zaune lafiya da juna a Najeriya, duk da rashin jituwa da ake kokarin haifarwa a tsakaninsu, amma malamai daga bangarorin biyu suna kokarin jan hankulan mabiyansu kan wajabcin zaman lafiya da juna.

 

https://iqna.ir/fa/news/3879374

Abubuwan Da Ya Shafa: najeriya jihar Kaduna coci kiristoci musulmi
captcha