IQNA

23:57 - February 17, 2020
Lambar Labari: 3484532
Tehran – IQNA, Bankin Sterling daya daga cikin bankunan Najeriya ya bayyana shirinsa na yin aiki da tsari irin na muslunci ga masu bukata.

Rahotanni daga Najeriya na cewa, a wani zama da aka gudanar a birnin Lagos cibiyar tattalin arzikin Najeriya, wasu manyan masu hannu da shuni a harkokin banki a Najeriya sun bayyana shirinsu na yin aiki da tsarin hada-hadar kudi ba tare da riba ba.

Shugaban bankin Sterling ya bayyana cewa, tuni suka fara aiwatar da irin wannan tsari ga masu bukata, kuma ya samu karbuwa matuka daga masu sha’aar hakan, yayin da kuam sauran harkokin banki suke tafiya kamar yadda suke bisa tsarin da aka saba.

Bashir Oshidi daya daga cikin manyan daraktocin bankin sterling ya bayyana cewa, bisa la’akari da bukatar da wasu adadi mai yawa na mutanen Najeriya suke da ita na son mu’amala ta banki ba tare da riba ba, wannan yasa suka dauki wannan mataki.

Kuma a cewarsa mutane da dama sun gamsu da hakan, inda hada-hadar banki ta karu matuka tun bayan bullo da wannan tsari ga masu bukata.

 

 

https://iqna.ir/fa/news/3879362

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: Naira ، Najeriya ، kudade ، hada-hada ، bankuna ، riba ، musulunci
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka: