IQNA

23:58 - March 06, 2020
Lambar Labari: 3484593
Tehran (IQNA) wani dan kunar bakin wake ya tarwatsa kansa da jigidar bam a gaban ofishin jakadancin Amurka a birnin Tunis na kasar Tunis.

Majiyoyin tsaro a kasar Tunisia sun sanar da cewa, wani dan ta’adda ya yi jigidar bama-bamai ya nufi ofishin jakadancin na Amurka, inda ya tarwatsa kansa a cikin jami’an tsaro da suke kusa da wurin.

Bayanin ya ce jami’in tsaro guda ya rasa ransa, wasu kuma sun samu raunuka sakamakon kai harin, kamar yadda shi ma dan ta’addan da ya tarwatsa kansa ya rasa ransa.

A daya bangaren kuma ofishin jakadancin kasar ta Amurka a birnin Tunis ya sanar da cewa, yana kira ga mutane da su kaurace wa wurin baki daya, domin bayar da dama ga jami’an tsaro su ci gaba da gudanar da bincike kan lamarin.

 

 

3883536

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: Tunisia ، ofishin jakadanci ، ، ، ،
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: