IQNA

22:59 - March 10, 2020
Lambar Labari: 3484609
Tehran - (IQNA) Antonio Guterres ya bayyana yunkurin yin kisan gilla a kan firayi ministan Sudan Abdullah Hamduk da cewa abin Allawadai.

Kamfanin dillancin labaran Anadolu ya bayar da rahotin cewa, a cikin wani bayani da kakakin babban sakataren majalisar duniya Stephane Dujarric ya karanta, ya bayyana cewa; Antonio Giterres ya nuna takaicinsa matuka kan yunkurin kisan Hamduk.

Ya ce, Guterres ya bayyana wanann yunkuri da cewa ba abu ne da majalisar dinkin duniya za ta amince da shi ba, kuma dole ne mahukuntan Sudan su binciko wadanda suke da hannu a cikin lamarin domin gurfanar da su a gaban kuliya.

A ranar Litinin da ta gabata ce dai aka kai wa tawagar firayi ministan Sudan Abdullah Hamduk harin bam a cikin birnin Khartum, inda ya tsallake rijiya da baya, amma wani daga cikin ‘yan tawagawar tasa ya samu raunuka.

 

3884429

 

Abubuwan Da Ya Shafa: MDD ، Sudan ، majalisar dinkin duniya
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: