IQNA

Sojojin Amurka Da Na Burtaniya Dari Hudu Da Hamsin Suka Isa Lardin Aden

22:51 - March 11, 2020
Lambar Labari: 3484613
Tehran (IQNA) sojojin Amurka da na Burtaniya su 450 sun isa lardin Aden da ke kudancin kasar Yemen.

Shafin yada labarai na Al-masa Press daga kasar Yemen ya bayar da rahoton cewa, sojojin Amurka da na Burtniya sun fara isa lardin Aden ne da nufin kafa sansanin soji mai karfi a yankin domin taimaka wa kawayensu.

Rahoton ya ce Amurka da Burtaniya suna da nufin jibge sojoji kimanin 3,000 a lardin Aden, kamar yadda kuma suke da niyyar kafa wasu sansanoni na dabana a cikin wasu yankuna na kudancin kasar Yemen.

Sojojin na Amurka da Burtaniya dai sun isa lardin aden ne tare da rakiyar wasu sojojin kasar hadaddiyar daular larabawa ne.

Amurka da Burtaniya suna bayyana cewa, maufarsu ta shiga yemen ita ce yaki da kungiyoyin ‘yan ta’adda masu tsatsauran ra’ayi, yayin dad a dama daga cikin al’ummomin suke ganin cewa maufar hakan ita ce aiwatar da wani sabon shiri na mamaye kasar, tare da haifar da matsaloli na tsaro, kamar yadda suka yi a Iraki, Afghanistan da sauransu.

 

 

3884580

 

 

captcha