IQNA

Cibiyar Hubbaren Imam Hussain Ta Mayar Da Martani Kan hare-Haren Amurka A Karbala

23:56 - March 13, 2020
Lambar Labari: 3484617
Tehran (IQNA) cibiyar da ke kula da hubbaren Imam Hussain (AS) ta yi tir da Allawadai da kakkausar murya kan harin da Amurka ta kaddamar kan filin jirgin Karbala.

Shafin Kamfanin dillancin labaran Saumaria News ya bayar da rahoton cewa, a cikin bayanin da cibiyar da ke kula da hubbaren Imam Hussain (AS) ta fitar, ta yi tir da Allawadai da kakkausar murya kan harin  Amurka a kan sabon filin jirgin Karbala, tare da bayyana hakan a matsayin babban laifi.

Haka nan kuma cibiyar ta bayyana cewa, wannan filin jirgi ne na farar hula da ba shi da wata alaka da ayyukan soji, wanda kuma kai masa hari da Amurka ta yi ya tabbatar da cewa tana yaki ne da al’ummar Iraki baki daya.

A daya bangaren kuma cibiyar ta bukaci da a hada dukkanin bayanai dangane da harinna Amurka a kan wannan filin jirgi da ake ginawa a halin yanzu, da kuma yadda ta kashe daya daga cikin masu aikin gininsa da kuma jikata wasu, domin gabatrwa ga bangaren shari’a.

 

3885032

 

 

 

captcha