IQNA

23:55 - March 14, 2020
Lambar Labari: 3484622
Tehran (IQNA) a cikin wani bayani da suka fitar, shugabannin larabawan Karbala a Iraki, sun jaddada cewa a shirye suke su koyawa Amurka darasi idan ta ci gaba da yi shishigi a kan al’ummarsu.

Shafin yada labarai na al'amalumah ya bayar da rahoton cewa, Sheikh Hussain Abbasi shugaban kabilun larabawan Bani Hassan, kuma daya daga cikin manyan dattijan karbala ya kashedi ga Amura, kan shishigin da take yi kan al'ummar Iraki, musamman a wurare masu alfarma.

Ya ce yana yin kira ga Amurka da ta kwana da sanin cewa, matukar dai ta zabi ta bude sabon shafin fito na fito da al'ummar Iraki, to kuwa za ta ga fito na fito daga al'ummar wannan kasa.

Wannan martani na zuwa ne kwana daya bayan harin da Amurka ta kaddamar kan filin jirgi na birnin karbala wanda ake cikin gina shi a halin yanzu, inda ta kashe wani ma'aikacin wurin da kuma jikkata wasu.

 

3885379

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: Karbala ، iraki ، shugabannin kabilun larabawa ، Amurka
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: