IQNA

23:56 - March 15, 2020
Lambar Labari: 3484627
Tehran (IQNA) minista mai kula da harkokin addini a kasar saudiyya ya bayyana cewa, idan ta kama za a iya rufe masallatai na wani dan lokaci.

Kamfanin dillancin labaran sputnik ya bayar da rahoton cewa, Abdullatif Bin Abdulaziz Al Sheikh minista mai kula da harkokin addini a kasar saudiyya ya bayyana cewa, idan ta kama za a iya rufe masallatai na wani dan lokaci saboda kauce wa yaduwar cutar corona.

Ya ce bisa ga fatawar malamai, bai halasta ba wanda yake dauke da wata cuta da mutane za su iya kwasa ya shiga cikin taron jama’a ba, kamar yadda bai halasta mai dauke da cutar corona ya halarci sallar jam’i a masallaci ba.

Haka nan kuma ya yi ishara da irin matakan da ake dauka a halin yanzu domin kual da masallatai, ta hanyar yin feshi na magunguna masu kashe kwayoyin cuta.

Sakamakon bullar cutar ta corona dai mahukuntan kasar ta Saudiyya sun dauki matakai na takaita taron jama’a a wuraren ibada musamman masallacin harami mai alfarma.

3885591

 

 

 

 

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: