IQNA

23:53 - March 16, 2020
Lambar Labari: 3484628
Tehran (IQNA) Mahukunta a kasar Morocco sun rufe masallatai da wuraren shakatawa a fadin kasar saboda yaki da yaduwar cutar corona.

Shafin yada labarai na tashar sky News arabi ya bayar da rahoton cewa, majalisar malaman addini ta kasar Morocco ta sanar a cikin wani bayani da ta fitar cewa, an rufe dukkanin masallatai da ake gudanar da salloli a kasar, domin kaucewa yaduwar cutar corona.

Kafin wannan lokacin ma’aikatar harkokin cikin gida ta kasar Moocco ta sanar da rufe dukkanin wuraren taruwar jama’a, da suka hada filayen wasanni, wuraren shakatawa da bude, da gidajen silima da sauransu.

Bayanin ma’aikatar harkokin cikin gidan kasar ta Morocco ya ce, wurare da ake sayar da kayayyakin bukatar rayuwar jama’a, da gidajen abinci da ake aikewa da shi, dokar ba za ta shafe su ba.

 

3885907

 

 

 

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: