IQNA

23:57 - March 25, 2020
Lambar Labari: 3484655

Ministan Tsaron kasar Sudan Ya Rasu A Yau

Teharn (IQNA) kakakin rundunar sojin Sudan ya sanar da cewa ministan tsaron kasar Jamaluddin Umar ya rasu.

Ministan Tsaron kasar Sudan Ya Rasu A Yau

Tashar Russia Today ta bayar da rahoton cewa, Laftanar Janar Jamaluddin Umar yana halartar wani taron tattaunawar sulhu tare da ‘yan tawayen Sudan a birnin Juba na Sudan ta kudu.

Rahoton ya ce, Umar ya rasu ne sakamakon tsayawar zuciyarsa daga aiki, kuma a halin yanzu haka na birnin na Juba ana gudanar da shirye-shiryen dauko gawarsa zuwa birnin Khartum.

Jamaluddin dai ya kasance tsohon shugaban hukumar leken asiri ta kasar Sudan a lokacin mulkin Umar Hassan Albashir, amma bayan hambarar da Albashir, Abdulfattah Burhan ya sanya a matsayin daya daga cikin mammbobin majalisar mulki ta kasar, daga bisani kuma ya ba mukamin ministan tsaro na kasar ta Sudan.

3887304

 

 

captcha