IQNA

OIC Za Ta Gudanar Da Zama Kan Batun Corona Ta Hanyar Yanar Gizo

23:54 - April 05, 2020
Lambar Labari: 3484680
Tehran (IQNA) mambobin kungiyar kasashen musulmi za su gudanar da zama ta hanyar yanar gizo domin tattauna batun corona.

Kungiyar kasashen musulmi ta sanar da cewa za ta gudanar da wani zaman gaggawa na musamman, domin tattauna batun corona da kuam yadda take ci gaba da yaduwa a cikin kasashen msuulmia  cikin wanann lokaci.

Babbar manufar taron dai ita ce duba halin da kasashen musulmi suke ciki dangane da batun na corona, da kuma duba yadda za su iya taimaka ma junansu a wanann bangare.

Yusuf Usaimin babban sakataren kungiyar ya bayyana cdwa, ganin cewa abu ne mai wuya a halin a iya gudanar da zaman tsakanin dukkanin mambobin kungiya, za a yi amfani da hanayar yanar gizo wajen gudanar da zaman.

Yanzu haka ana tatatunawa tsakanin mambobin kungiyar yadda za a gudanar da zaman, da kuma muhimman abubuwan da za a tattauna a tsakaninsu.

 

3889400

 

 

 

captcha