IQNA

Guterres Ya Ce Da Hadin Kai Ne Za  A Iya Karya Corona

23:59 - April 11, 2020
Lambar Labari: 3484702
Tehran (IQNA) babban sakataren majalisar dinkin duniya Antonio Guterres ya bayyana cewa idan al’ummomin duniya suka hada kai za su iya kawar da corona.

A cikin wani sako da ya aike na easter, Antonio Guterres ya bayyana cewa wanann lokaci ne da mabiya addinin kirista da yahudawa suke gudanar da bukukuwan easter, yayin da nan ba da jimawa ba musulmi za su shiga watan Ramadan.

Ya ce wannan lokaci ne mai matukar muhimmanci ga dukkanin mabiya addinai a duniya, domin kuwa lokuta ne masu albarka.

Ya ce idan dukkanin al'ummomin duniya suka hadu suka za su iya taka rawa wajen karya annobar corona, tare da karfafa masana masu hankoron samar da maganin cutar, da kuma kiyaye ka'idoji da jami'an kiwon lafiya suke bayyanawa.

3890889

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
captcha