Tehran (IQNA) Sheikh Muhammad Mahmud Usfur makarancin kur’ania gidajen radiyo da talabijin na Masar ya rasu a jiya bayan fama da rashin lafiya.

Sheikh Muhammad Usfur daya ne daga fitattun makarantan kur’ani da suka shahara a wanda aka haife a shekarar 1938 kasar Masar, inda gidajen radiyo da talabijin na kasar suke sanya karatunsa da kuma addu’oinsa. Yayi karatu a wajen marigayi sheikh Mahmud Alanusi.