IQNA

23:57 - April 23, 2020
Lambar Labari: 3484738
Tehran (IQNA) sakamakon barazanar da Trump ya yi kan cewa ya bayar da umarni da a tarwatsa jiragen ruwa idan sun kusanci jiragen ruwan Amurka, Iran ta kirayi jakadan Switzerland a Tehran.

Kwana guda bayan barazanar da shugaba Donald Trump, na Amurka ya yi wa Iran ne cewa ya bada umarnin tarwatsa duk wani jirgin ruwa da ya yi wa sojojin Amurka barazana a tekun Fasha, Ma’aikatar harkokin wajen Iran, ta kirayi jakadan kasar Switzerland, a birnin Tehrandomin bayyana masa bacin rai kan abunta ta kira takala daga Amurka.

Kasar Switzerland, ita ce ke wakiltar harkokin da suka shafi Amurka a Iran.

Ma’aikatar harkokin wajen kasar ta Iran, ta bakin kakakinta, Abbas Moussavi, ta ce, an gayyaci jakadan na Switzerland, ne domin sanar da shi bacin ran Iran, game da takalar sojojin ruwan Amurka a tekun Fasha.

Mista Moussavi, ya yi tir da abunda ya ce ya sabawa dokoki da kuma tsokana ta sojojin Amurka a kusa da ruwan Iran, wanda ya ce ba makawa Iran za ta yi duk abunda ya dace domin kare ruwanta sannan zata mayar da martani kan duk wani irin mataki.

A ranar Laraba ne shugaban Trump, ya wallafa a shafinsa na tweeter cewa ya baiwa sojojin runwan kasarsa na US Navy, umarnin tarwatsa duk wani jirgin ruwna Iran, da ya kawo masu tarnaki ko barazana a Tekun na fasha.

 

3893699

 

 

 

 

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: bacin rai ، bayyana ، masa ، Iran ، jakadan ، kasar ، switzerland
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: