IQNA

23:59 - April 23, 2020
Lambar Labari: 3484739
Tehran (IQNA) wasu daga cikin kasashen musulmi da suka hada da Saudiyya sun sanar da ganin watan ramadan mai alfarma.

Kasashen Saudiyya, Tunisia, Kuwait, Bahrain, Yemen, Turkiya, Darul Ifta Lebanon, UAE, Qatar, da wakafin Sunni a Iraki, sun sanar da gobe Juma’a 24 ga watan Afirilu a matsayin ranar daya ga watan Ramadan mai alfarma.

Hukumomi a Saudiyya, sun sanar da hango jinjirin watan Ramadana da yammacin ranar Alhamis, wanda ya kawo karshen watan Sha’aban.

Hakan dai ya sanya Juma’a ranar farko ta watan azumin Ramadana a Saudiyya.

Bana dai za’a gudanar da azumin a cikin wani irin yanayi da ba’a taba fuskanta ba sakamakon annobar coronavirus a duniya.

Kafin hakan dama a Saudiiya Babbar majalisar koli ta malamai ta bukaci al'ummar Musulmin duniya a kasashen da ke fama da cutar korona su yi Sallah a gidajensu lokacin watan Azumin Ramadan.

Malaman sun ce: "Ya kamata musulmi su zama abin misali ta hanyar gudanar da addininsu yayin da suke kiyaye matakan kariya da hukumomi suka dauka a kasashen da suke," in ji sanarwar.

Sannan majalisar ta bukaci musulmi su kauracewa duk wani taro a lokacin buda-baki ko sahur a cikin Azumi.

3893708

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: kasashen musulmi ، watan ramadan ، mai alfarma ، gobe ، ،
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: