IQNA

Mai Yiwuwa A Bude Haramomi Biyu Masu Alfarma

22:20 - April 29, 2020
Lambar Labari: 3484755
Tehran (IQNA) Sheikh Abdulrahman Al-sudais mai kula da haramin Makka da Madina ya bayyana cewa, mai yiwuwa a bude masallatan biyu a nan gaba.

Shafin yada labarai na Arabi 21 ya bayar da rahoton cewa, Al-sudais ya bayyana cewa, an dauki matakin rufe wadannan wurare biyu masu alfarma sanadiyyar bullar annobar da ake fama da ita, domin kare lafiyar jama’a masu gudanar da ibada a wurin.

Ya ce a halin yanzu za a ci gaba da bin matakan da aka dauka na kare lafiyar jama’a da kuma tabbatar da cewa an yi biyayya ga dukkanin umarnin da jami’an kiwon lafiya suka bayar.

Kafin wannan lokacin Hani Bin Hasani Haidar kakakin cibiyar kula da haramin Makka da Madina ya sanar da cewa, wadannan wurare biyu za su ci gaba da kasancewa  a karkashin kula da kuma kaucewa duk wani abin da zai iya cutar da jama’a.

A cikin sa’oi 24 da suka gabata cutar covid-19 ta ta sake kama mutane dubu 1 da 266 a kasar Saudiyya, yayin da jimillar wadanda suka kamu adadisu ya kai 20, 077, sai kuma mutane 152 sun riga gidan gaskiya.

 

3895225

 

captcha