Shafin yada labaran yaum sabi ya bayar da rahoton cewa, a jarabawar da aka gudanar ta zaben makaranta mafi kyawun sauti domin addu’oi da karatun kur’ani a radiyon kur’an, a tsakanin mutane 200 da suka halarta, an zabi Muhammad Adel Alasar dan shekaru 13 a matsayin wanda ya lashe jarabawar da aka yi.
An zabe shi domin gudanar da karatun kur’ani da kuma karatun addu’oin watan Ramadan da sauran ranaku da ake gudanar da addu’oi na musamman, gami da karatun kur’ani mai tsarki.
Gidan radiyon kur’ani na Masar ya dauki alkawalin daukar nauyinsa domin ci gaba da karatu, a daya bangaren kuma a matsayin ma’aikacin gidan radiyon na kur’an.