IQNA

Wasikar Zarif: Ya Kamata Kwamitin Tsaro Ya Yi Allawadai Da Takunkuman Amurka Kan Iran

23:51 - May 09, 2020
Lambar Labari: 3484780
Tehran (IQNA) Ministan harkokin wajen kasar Iran Muhammad Jawad Zarif ya aike da wata wasika zuwa ga babban sakataren majalisar dinkin duniya Antonio Guterres dangane da yadda Amurka take yi fatali da dokokin kasa da kasa.

A cikin wata sanarwa da kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran ya fitar a yammacin jiya Ministan harkokin wajen kasar Iran Muhammad Jawad Zarif ya aike da wata wasika zuwa ga babban sakataren majalisar dinkin duniya Antonio Guterres dangane da yadda Amurka take yin fatali da dokokin kasa da kasa, daga cikin har yadda ta yi fatali da yarjejeniyar da aka cimmawa tsakanin manyan kasashen duniya kan shirin Iran na nukiliya.

Ya ce, a cikin wasikar ta Zarif, ya ja hankalin babban sakataren majalisar dinkin duniya da ya sauke nauyin da ya rataya a kansa na tabbatar da cewa dukkanin kasashen duniya sun yi aiki da dokokin da suka rattaba hannu kansu a karkashin majalisar dinkin duniya.

Zarif ya kara da cewa Amurka tana yin barazana ga zaman lafiyar duniya baki daya, ta hanyar yin katsalandan a cikin harkokin kasashen duniya, tare da haddasa fitintinu a tsakanin al’ummomi, wanda hakan yake bukatar yunkuri daga dukkanin kasashe domin taka mata burki.

Haka nan kuma Zarif ya jadda cewa maimakon nuna cewa kasashen duniya suna tare da Iran kan batun shirin nukiliya, ya kamata kuma alokaci guda kwamitin tsaron majalisar dinkin duniya ya yi Allawadai da takunkuman Amurka a kan Iran.

Ya kara da cewa wadannan takunkumai ba su da banbanci da laifukan yaki a  kan bil adama, wadanda suka cancanci yin tir da Allaadai da su.

3897491

 

 

captcha