Sami Alqasemi babban daraktan ma’aikatar kula da harkokin addini a kasar Tunisia ya bayyana cewa, batun bude masallatai a kasar a dararen laitul Qadr ya dogara ne da mahangar ma’aikatar kiwon lafiya ta kasar.
Alqasemi ya ce akwai bukatu da dama da ‘yan kasar suke gabtar masa domin ganin an bude masallatai a dararen laitul qadr domin mutane su samu damar yin ibada a cikinsu, inda ya ce yana yin dubi kan hakan.
Ya kara da cewa, tun bayan da aka rufe masallatai a kasar Tunsia, ma’aikatarsa ta dauki matakin yin feshin magungunan kashe kwayoyin cutta a dukkanin masallatan kasar.