A cikin bayanin da kwamitin kare hakkokin musulmi a kasar Burtaniya ya fitar a jiya, ya sanar da cewa,tun bayan da aka samu wasu ‘yan jam’iyyar Consevative na yin kalaman batunci da nuna kiyayya ga musulmi da muslunci, kwamitin kare hakkin bil adama na kasar Burtaniya bai dauki wani mataki kan hakan ba.
Bayanin ya ce, kwamitin kare hakkokin musulmi na kasar Burtaniya ya gabatar da rahotanni daban-daban dangane da wannan batu, amma kuma har yanzu ba a gudanar da bincike kan rahoton da aka gabatar ba.
Kwamitin kare hakokin musulmin ya yi zargin cewa, akwai hadin baki tsakanin jam’iyyar Consevative mai mulki a halin yanzu a Burtaniya, da kuma kwamitin kare hakkin bil adama na kasar, domin kuwa a shekarar da ta gabata an zargi wasu ‘yan jam’iyyar adawa ta Labour, da nuna kin jinin yahudawa, kuma ba tare da bata lokaci ba kwamitin ya bude bincike kan batun.