IQNA

23:56 - May 15, 2020
Lambar Labari: 3484801
Tehran (IQNA) mayakan sa kai na al’ummar Iraki sun kori ‘yan ta’addan Daesh daga wasu yankuna na kasar Iraki.

Kamfanin dillancin labaran Samirra ya bayar da rahoton cewa, dakarn hashd sha’abi sun samu nasarar fatattakar mayaan kungiyar ‘yan ta’addan Daesh daga yankin Samirra a cikin gundumar Salahuddin a yammacin kasar.

Bayanin ya ce dakarun sa kan sun samu nasarar halaka wasu daga cikin ‘yan ta’addan yayin da sauran suka tsere zuwa wasu yankuna da ke kan iyakar kasar ta yamma.

Kafin wannan lokacin Ali Hussaini daya daga cikin kwamandojin dakarun sa kai na al’ummar ya sanar da cewa, sun halaka ‘yan ta’addan Daesh kimanin hamsin da suka fito daga kasashe daban-daban a cikin lardin na Salhuddin.

 

3898868

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: mayakan sa kai ، Iraki ، hashd sha’abi ، ، ،
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: