IQNA

23:55 - May 16, 2020
Lambar Labari: 3484806
Tehran (IQNA) Cin zarafin da tashar MBC mallakin gwamnatin Saudiyya da ke watsa shirinta daga Dubai UAE, ta yi wa shahid Abu Mahdi Al-muhandis ya fusata al’ummar kasar Iraki matuka.

Kamfanin dillancin labaran saumaria News ya bayar da rahoton cewa, kwamitin kula da harkokin sadrawa da yada labarai a majalisar dokokin kasar Iraki, ya yi Allawadai da kakkausar murya kan cin zarafin da tashar MBC ta yi wa shahid Abu Mahdi Al-Muhandis, inda tashar ta kira shi da sunan dan ta’adda.

Kwamitin ya ce yana kiran wannan tashar talabijin da ta gaggauta neman afuwar al’ummar Iraki baki daya, idan kuma ba haba, to za a rufe dukkanin ofisoshin da tashar take da su a fadin kasar Iraki, kuma za a haramta ayyukanta baki daya  a cikin kasar.

Bayanin kwamitin ya ce; Al-Muhandis mutum ne da ya sadaukar da rayuwarsa baki daya domin yi wa al’ummar kasar Iraki hidima tsawon shekaru, kamar yadda kuma shi ne gishikin kafa rundunar sa kai ta al’ummar Iraki wato dakarun Hashd Al-sha’abi, wadanda suka fatattaki ‘yan ta’addan Daesh kuma suka karya lagonsu a Iraki.

Su a nasu dakarun sa kai na Hashd Al-sha’abi a Iraki sun kirayi gwamnatin kasar da ta dauki matakin gagawa kan wannan lamari, domin kawo karshen irin wannan cin fuska da tashoshin kasashe masu daukar nauyin ‘yan ta’adda suke yi a kan jagorin dakarun Hashd Al-sha’abi na Iraki.

 

https://iqna.ir/fa/news/3899229

Abubuwan Da Ya Shafa: dauki ، matakin ، gwamnatin kasar ، Iraki ، hashd sha’abi ، daesh
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: