IQNA

An Yi Allawadai Da Kasashen Turai Da Suka Keta Alfarmar Iraki

23:02 - May 18, 2020
Lambar Labari: 3484810
Tehran (IQNA) bangarorin siyasar Iraki da dakarun sa kai na kasar sun bukaci kasashen turai da suka daga totocin masu auren jinsi da su bar kasar.

Shugaban gammayar kungiyar Fatah ta kasar Iraki ya mayar da matani mai zafi game da matakin da ofisoshin jakadancin kungiyar tarayyar turai da na kasashen Ingila da Kanada suka dauka na daga tutar masu nuna goyon bayan Auren jinsi a birnin Bagadaza .

kuma ya bayyana shi a matsayin abin kunya ne da ya a sabawa alada da kyawawan halaye da tsarin zamantakewar alummar kasar.

Har ila yau ya kara da cewa mun yi tir da duk wani mataki na cin zarafin Addini da alummar kasar suka yi imani da shi, kana ya bukaci gwamnatin kasar da ta gaggauta korar jakadun kasahen guda 3 da suka aikata wannan danyen aiki daga kasar iraki , domin Irakawa basu amince da su a matsayin jakadun kasashensu ba.

Daga karshe ya nuna cewa daukar wannan mataki ya zama dole musamman idan aka yi la’akari da yadda suka keta hurumun watan mai Alfarma na Ramadana da kuma cin zarafin abubuwan da miliyoyin Irakawa suka yi Imani da shi.

 

 

3899648

 

captcha